✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da aminin mahaifin yarinya kotu kan zargin yi mata ciki

Majalisar Zartarwar Mata ta Najeriya National Council For Women Society of Nigeria (NCWS) reshen Jihar Yobe, ta maka wani magidanci mai suna Alhaji Dauda Mubi…

Majalisar Zartarwar Mata ta Najeriya National Council For Women Society of Nigeria (NCWS) reshen Jihar Yobe, ta maka wani magidanci mai suna Alhaji Dauda Mubi mai shekara 55 a kotu bisa zargin cin amanar marigayin abokinsa wajen yi wa ‘yarsa mai shekara 13 ciki, wacce aka sakaya sunanta.

Jim kadan bayan kammala zaman kotun, Shugabar Majalisar Zartarwar Mata ta Jihar Yobe, Hajiya Halima Joda Kyari, ta shaidawa Aminiya yadda lamarin ya faru, inda ta ce wanda ake zargin Alhaji Dauda aminin mahaifin yarinyar da ake zargin ya yi wa cikin ce, kuma tun bayan rasuwar mahaifin yarinyar ta ke gaban mahaifiyarta, inda shi Alhaji Dauda yake ci gaba da kulawa da wasu dawainiyoyinsu na rayuwa.

Halima Joda ta ce “Alhaji Dauda Mubi da yarinyar dukkansu mazauna Unguwar Mubi ne a Karamar Hukumar Fika ta jihar Yobe kuma a cewarta ya yi amfani da wata dama ce a matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a yankin, kuma yake ganin kamar kowa na tsoronsa, ya rika yin lalata da yarinyar akai-akai har sai da ta yi ciki, saboda gadarar babu yadda suka iya da shi,” inji ta.

Ta kara da cewa “Da muka ga ciki ya bayyana a jikin yarinyar ne har ya kai watanni biyar, hakan tasa mahaifiyar yarinyar ta kai rahoto ga kungiyarmu ta NCWS dake Fika, inda mu kuma muka maka shi a kotun Majistare na garin Fika da nufin a bi kadun yarinyar.”

“Amma kafin a shiga kotun ya nemi a sasanta, ba sai an je kotu ba, da suka ki yarda sai ya yi kokarin ya gudu daga garin baki daya, amma kuma a yayin gudun ne ya samu hadari, inda ya karye a kafa,” In ji ta.

Bayan shigar da kara da fara shari’ar ne Alkalin Kotun, Mai Shari’a Muhammad Y. Alagarno ya ba  da umarnin a dora karayar da wanda ake zargin ya samu, sannan ya tura shi zuwa gidan kaso don jiran ranar 29 ga wannan watan don ci gaba da shari’ar.