✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano yaro da ransa a cikin katanga

  A makon jiya ne al’ummar unguwar Oduduwa a Jihar Ondo suka wayi gari da labari mai matukar al’ajabi bayan da aka gano yaro dan…

 

A makon jiya ne al’ummar unguwar Oduduwa a Jihar Ondo suka wayi gari da labari mai matukar al’ajabi bayan da aka gano yaro dan shekaru 12 makale a tsakanin ginin katanga ta bulo.

Mutanen da ke makwaftaka da ginin katangar da aka ciro yaron sun shaida cewa sun ta jiyo wani irin kuka daga ginin katangar har na tsawan kwanaki uku, inda hakan ya sanya suka yanke shawarar fasa katangar, har suka ci karo da yaron dan shekaru 12, wanda suka fito da shi a sume, kafin daga bisani aka watsa masa ruwa har ya farfado.
Wani dattijo mazaunin Ondo, mai suna Femi Babalola ya shaida wa Aminiya cewa, katangar da aka gano yaron ba ta da nisa da wani gidan tsafi da ke unguwar Oduduwa. Don haka akwai alamun yaron matsafa ne suka yi tsafi da shi, suka yi suddabarun cusa shi a katangar, ta hanyar mayar da shi karamar dabba, bayan da Allah ya yi da sauran kwanansa a gaba ne tsafin ya karye, ya komo siffarsa ta asali, har ya samu damar yin kuka jama’ar wajen suka jiyo shi, suka kai masa ɗauki.
“Idan ka lura da ginin katangar da aka ciro yaron za ka tabbata cewa, shekarunta sun fi na yaron, ka ga babu maganar a ce an yi ginin da shi a ciki ne, wannan aiki ne na matsafa, wanda ba kuma bakon abu ba ne a wannan yanki. Don kimanin shekaru 15 ke nan da aka gano wata mata da ranta a jikin ginin rijiyar wani gida a garin Ibadan,” inji shi.
Sunan da unguwar da aka gano yaron ta ci, wato Oduduwa, suna ne na wani mutum da Yarbawa suka yi ittifakin zuri’ar su kaf daga gare shi ta samo asali. Kuma masu bin addinin tsafinsu na gargajiya sun yi imanin shi ne farkon halite, wanda ubangiji ya turo shi daga sama dauke da zakara a hannunsa, wai da zakaran ya yi amfani ya shimfida kasar duniya baki dayan ta bayan da ya tarar da ita malale da ruwa.
Ga duk mutumin da yake zaune a Kurmi, musamman a Kudu maso Yamma gidajen matsafa ba bakon abu ba ne a gare shi. Don akwai gidajen da suke kulle babu kowa, ba kuma wanda ya isa ya shige su sai cikakkun matsafa, waɗanda kan shiga sau daya a duk shekara.