✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano yaran da suka kwana 40 suna cin ciyayi a raye a Colombia

Sun shafe sama da kwana 40 suna cin ciyayi a daji

Shugaban Kasar Colombia, Gustavo Petro ya sanar da gano wasu yara ’yan asalin kasar hudu da suka bace sama da wata guda a dajin Amazon na kasar.

Yaran sun bace ne tun bayan wani karamin jirgin saman da suke ciki ya yi hatsari.

Da yake yi wa manema labarai karin haske, Shugaban Kasar, Gustavo Petro yace an ga abin mamaki ranar Juma’a, lokacin da jami’an saro sama da 200 da aka baza a dajin na Amazon suka gano yaran.

Sama da kwana 40 ke nan da bacewar yaran, kuma tsawon lokacin sun rika cin ciyayi da ganyayyaki domin su rayu.

Ya ce yaran na cikin alamun tagayyara, amma suna samun kulawar likitoci.

Yaran ’yan gida daya – masu kimanin shekara 13 da 9 da kuma 4 da kuma 1, sun ja hankali sosai a yunkurin ceto su da gwamman sojoji ke yi a dajin.

(RFI Hausa)