✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano yara 2 da aka sace a Gombe a Anambra

An gano wasu yara 2 da aka sace daga jihar Gombe aka kaisu jihar Anambra, kuma an mayar dasu ga iyayensu. Yaran dai an sace…

An gano wasu yara 2 da aka sace daga jihar Gombe aka kaisu jihar Anambra, kuma an mayar dasu ga iyayensu.

Yaran dai an sace su ne lokacin da suke wasa tare da wasu yara a gidajen iyayensu, inda aka kama wasu mutum uku da hannun su a satar yaran, wadanda suka hada da: Patience Opia daga jihar Kuros Ribas da Ejece Obi daga jihar Anambra, sai kuma Blessing John daga jihar Bauchi.

An kama wadanda ake zargin ne kamar yadda Kwamishinan ’Yan sanda na jihar Anambra, John Abang, ya sanar ta bakin Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’yan sanda, Haruna Mohammed, an kama barayin yaran ne a jihar ta Anambra bisa binciken kwakwaf da rundunar tayi, yayin da ya ce tuni barayin sun fara yunkurin siyar da kowanne daga cikin yaran a kan kudi Naira dubu 750.

Ya ce, daya daga cikin barayin yaran, Blessing John, ta yi karyar cewar daga cikin yaran dan cikinta ne, inda kuma ta ce daya yaron dan kanwar tane. Tuni dai an mika yaran ga iyayensu, bayan da binciken rundunar ya tabbatar dasu.