An kama wata mata mai cutar coronavirus a yayin da take tsaka da cin kasuwa bayan ta tsere daga hannun hukuma.
Aminiya ta gano cewa cewa an fara neman matar ne ruwa a jallo tun da ta saci jiki ta tsere jim kadan bayan gwajin coronavirus da aka yi mata a jihar Imo ya tabbatar tana da cutar.
Matar wadda ba a bayyana sunanta ba ta gudu ne zuwa jihar Ondo inda ta ci gaba da harkokinta kamar yadda ta saba, ba tare da ta killace kanta ko ta mika kanta ga mahukunta ba.
Da yake tabbatar da hakan, Kwamishinan Lafiya na jihar Ondo Dokta Wajaba Adgbenro ya ce an gano matar ne tana tsaka da sayar da kayan gwanjo a Babbar kasuwar Oja-Oba da ke garin Akure.
Kwamishinan ya ce tun bayan da matar ta sulale daga jihar Imo mahukunta a jihar Imo da kuma Ondo suka shiga neman ta ruwa a jallo.
Ya kara da cewa an fara aikin killace mutanen da suka yi mu’amala da ita, ciki har da iyalanta da abokan cinikayyarta da kuma makwabtanta.
Zuwa ranar asabar, 6 ga watan Yuni mutum 41 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a jihar ta Ondo.