✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano kogin ruwan sanyi da na zafi a Kurosriba

An gano wani kogi a garin Ugep, hedkwatar karamar Hukumar Yakurr, Jihar Kurosriba mai abin al’ajabi, wanda ruwansa rabi na dumi ne, daya rabin kuma…

An gano wani kogi a garin Ugep, hedkwatar karamar Hukumar Yakurr, Jihar Kurosriba mai abin al’ajabi, wanda ruwansa rabi na dumi ne, daya rabin kuma na sanyi. Duk mutumin da ya shiga kogin domin yin wanka, zai ji haka a jikinsa.

Basaraken Ugep, Obol Ofem Ubana Eteng ne ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa.

Kamar yadda binciken Aminiya ya gano, idan banda ruwan da ke bulbulowa daga kogin Ikogosi na Jihar Ekiti, wanda shi ma ke da irin wannan yanayi na rabi ruwan sanyi, rabi na dumi, ba a samu na biyunsa ba sai kwanan nan a Ugep. 

Aminiya ta tambayi Basarake Obol, ko yaya ma aka yi aka gano ruwan kuma waye ya gano shi, ya sanar wa masarautasa? Sai ya ce: “Wani mafarauci ne da ke yawon farauta ya gano shi, ya kuma garzayo ya sanar mana cewa ya ga wani kogi mai rabi ruwan sanyi rabinsa kuma na dumi.”

Wakilinmu ya zanta da wasu da suka shiga kogin suka yi kurme, don gani da jin kwakwaf yadda ruwan yake. Yawancin wadanda aka zanta da su, sun gaskata labarin; sun ce tabbas babu karya.