✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano budurwar da aka sace a Abuja a Anambra

Lauratu Lawal, buduruwa mai shekara 17 da a ke zargin wani surukin mahaifinta da bacewarta a Garin Dakwa Abuja, ta bayyana a garin Anacha ta…

Lauratu Lawal, buduruwa mai shekara 17 da a ke zargin wani surukin mahaifinta da bacewarta a Garin Dakwa Abuja, ta bayyana a garin Anacha ta jihar Anambra bayan sama da wata daya da aukuwar lamarin.

Wani makusancin yarinyar, ya shaidawa Aminiya a safiyar yau Laraba cewa tini ‘yan sanda su ka taho da ita zuwa Abuja daga yankin a daren ranar Talata.

Ya ce, bayan isowar tasu, an nemi iyayen yarinyar a hedikwatar ‘yan sanda ta Abuja, inda su ka je don karbarta a safiyar ta yau Laraba.

Idan dai za a tuna Aminiya ta bada labarin kama surukin mai suna Jibrin Abubakar da a yanzu haka ake tsare da shi a cibiyar ‘yan sanda ta SARS ta Abuja kan lamarin.

Cikakken rahoton kan yadda a ka ganota na nan tafe a jaridar AMINIYA da ke fitowa a ranar Juma’a.