✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fito da sabon tsari a Gasar Zakarun Kulob Na Turai

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta ce daga kakar wasa ta 2018 zuwa 2019 za ta fara amfani da sabon tsarin shiga…

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta ce daga kakar wasa ta 2018 zuwa 2019 za ta fara amfani da sabon tsarin shiga gasar a Nahiyar Turai.

Sabon tsarin da Hukumar ta fito da shi ya nuna kungiyoyin kwallon kafa hudun da suka kasance a saman teburin Gasar firimiyar Ingila da gasar La-Liga ta Sifen da Gasar Serie A ta Italiya da kuma Gasar Bundesliga ta Jamus za su haye gasar kai tsaye ba tare da na hudun sun yi wasan cancantar shiga gasar ba (Play-off).

A da kungiyoyin da suka kasance na hudu a wadannan gasanni sai sun yi wasa gida-da-waje (Play-off) da kungiyoyin da za a hada su kafin su haye gasar, amma yanzu abin ya kau.

Rahboton ya nuna kungiyoyin da suka fito daga Ingila ne za su fi amfana da wannan sabon tsari.

Sannan hukumar ta ce kulob din da suka kasance na 5 da na 6 a gasannin kasashen da aka lissafa a sama su ma za su haye gasar zakarun Europa ne kai tsaye ba tare da sun yi gasar cancanta (Play-off) ba.  Haka kuma hukumar ta ce za a samu canjin lokacin da ake buga gasar inda daga kakar wasa ta 2018-2019 wasannin za su rika gudana ne a tsakanin karfe 5 da kwata zuwa karfe takwas na dare agogon Najeriya, ba kamar yadda ake yi a halin yanzu na a wasu lokutan akan kai karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya kafin a fara gasar idan aka kai wani mataki ba.