An fitar da jerin sunayen za a dauka aiki a matakin hafsa da kananan jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).
Hukumar ta fitar da sunayen ne a ranar Asabar tare da shawartar masu neman gurabun aikin da su ziyarci shafinta, wato www.ndlea.gov.ng domin duba sunayensu da cibiyoyin da za su halarta da ranakun da za a tantance su.
- ’Yan fashi sun tare motar banki, sun daka wa kudin cikinta wawa
- Kwankwasiyya: Ana zargin Dangwani da zagon kasa
- Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
- Matasa sun hallaka ’yan bindiga a Sakkwato
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce za a gudanar da tantancewar ce a rukuni-rukuni a cibiyoyi da kuma ranaku daban-daban.
Ya ce wajibi ne mutanen su halarci cibiyoyin da takardun shaidar mai tsaya musu, takardun haihuwar da kuma na shaidar karatu na ainihi da kuma kwafinsu.
Za kuma su je da takardar shaidar jihar da suka fito da ta shaidar koshin lafiya daga asibitin gwamnati.
Ana kuma so su halarci cibiyoyin ne sanye da fararen gajerun wanduna da rigunan ‘T-shirt’ da takalman kambas da safuna —duk farare.
Sanarwar ta kara da cewa duk wanda bai kiyaye wadannan ka’idojin da aka gindaya ba, to shi da kansa ya kayar da kansa nan take.