✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar Kokawa a Nijar

A ranar Larabar makon jiya ne aka bude gasar fitar da wakillan da za su shiga gasar wasan kokawar gargajiyar ta shekarar 2014 kamar yadda…

A ranar Larabar makon jiya ne aka bude gasar fitar da wakillan da za su shiga gasar wasan kokawar gargajiyar ta shekarar 2014 kamar yadda ake yi a duk  shekara a kasar Nijar.
Bude wannan wasa da aka yi a filin wasan kokowar gargajiya da ke unguwar Bukkoki a cikin birnin Yamai ya nuna an fara da fitar wakillan a sauran jihohi 8 da kasar take da su. Kamar yadda Daraktan al’adu da wasannin motsa jiki a birnin Yamai, Lauwali Garba Mahamad ya shaida, “zamowar Yamai babban birni na kasa shi ya sa ta kasu zuwa rukunnai tun daga na daya har zuwa na biyar,wadanda daga cikinsu ne za a zakulo ’yan wasa mutun 60 har ila yau a cikinsu ne kuma za a fitar da mutun 16 da su ne za su tafi jahar da za a gudanar da gasar wadda a bana za ta gudana ne a Jihar Diffa a watan Maris”.
Daraktan ya kara da cewa, haka su ma sauran jihohin za su gudanar da nasu kamar yadda aka yi a Yamai.
Lauwali ya ce, za a samu ‘yan wasa 128 da za su hadu don fitar da zakaran da zai lashe Takobin da ake azawa don cinsa.
Ita dai kasar Nijar ta zamo ta biyu a wajen gudanar da wasan kokowar gargajiya a tsakanin kasashen Afirika yayin da  Senegal ce ke kan gaba. Shi dai wannan takobi da za a yi gasar a kansa a halin yanzu yana Jihar Zinder wadda ita jahar da ta lashe shi a shekarar 2013 ta hannun dan wasanta mai suna Aliyu Sallau sakamakon hukuncin da alkalan wasan suka yanke na gaza samun wanda ya yi nasara a tsakanin dan kokowar da ya wakilci Jihar Maradi da na Yamai wanda shi na Zinder yake jiran dayansu. Alkalan dai sun yanke hukuncin ‘yan kokowar biyu sun yi mutuwar tsaye wanda hakan ne ya sa Aliyu ya lashe takobin.