✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure wadda ta saci yara shekara 9

Babbar Kotun Jihar Kano ta 11 a karkashin jagorancin Mai shari’a A’isha Muhammad ta yanke wa matar nan mai suna Lobe Ogar hukuncin daurin shekara…

Babbar Kotun Jihar Kano ta 11 a karkashin jagorancin Mai shari’a A’isha Muhammad ta yanke wa matar nan mai suna Lobe Ogar hukuncin daurin shekara tara a kurkuku babu zabin biyan tara bisa samunta da laifin satar yara uku.

Kotun ta kuma umarce ta ta biya Naira dubu 250 ga iyayen yaran don rage musu radadin da suka shiga.

Tun a shekerar 2014 ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta kama matar lokacin da ta saci yara uku daga Hotoro a Kano tana yunkurin tsallakewa da su zuwa Abuja don mika su ga wadanda suka ba ta kwangilar sato yara don tsafi da su. Asirin matar ya tonu ne a lokacin da yaran suka rika  kuka lamarin da ya ja hankalin direban motar haya da Lobe Ogar ke ciki inda ya sanar da jami’an tsaro su suka kama ta.

Lokacin shari’ar Lauyan Gwamnati, Barista Lamido Sorondinki, ya gabatar da shaidu biyar kuma ya bayyana gamsuwa da hukuncin da kotun ta yanke.

Lauyan kariiya Barista Abdullahi Ya’u Rjiyar Lemo, ya ce, “Za mu sake karanta hukuncin idan mun ga akwai bukatar daukaka kara za mu yi musamman ganin wannan ne hukuncin kotu na farko.”

Daya daga cikin iyayen yaran mai suna Kamilu Muhammad ya ce ba su gamsu da hukuncin kotun ba.