✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ta saboda gaza biyan kudin fansar kanta

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kumbotso a Jihar Kano ta bayar da iznin sakaya wata matar aure mai suna Maryam Ahmad bisa laifin gaza…

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kumbotso a Jihar Kano ta bayar da iznin sakaya wata matar aure mai suna Maryam Ahmad bisa laifin gaza biyan kudin aurenta don fansar kanta daga mijinta.

Tunda farko mijin matar ne ya kai kara gaban kotun yana neman kotun a tilasta matar tasa ta biya shi kudaden da ya kashe wajen aurenta wanda suka yi zaman kwana 16, inda ta nuna cewa ba za ta kara zama da shi a matsayin miji ba.

A zaman kotun na farko wanda aka yi kimanin makonni shida da suka gabata, kotun ta waiwayi Maryam kan dalilinta na son rabuwa da mijin nata inda ta bayyana cewa mijin nata yana dukanta har ma ya kai ya fara shake mata wuya haka kuma a cewarta yana kulle ta a duk lokacin da zai fita.

Bayan kotu ta saurari bangarorin guda biyu sai ta yanke cewa Maryam za ta biya mijin nata kudin aurensa Naira dubu 90 a matsayin fansar kanta.

A zaman da aka sake yi ranar Larabar makon jiya kuma Maryam ta kai wa kotu Naira dubu 45 daga cikin kudin, inda kotu ta ba ta wa’adin mako guda ta kawo cikon Naira dubu 45.

Sai dai a zaman kotun da aka yi a ranar Larabar da ta gabata Maryam ta kai wa kotu Naira dubu 13 ne tare da alkawarin za ta ciko ragowar kudin a karshen watan Nuwamba, a cewarta iyayenta ba su da halin biyan kudin gaba daya, saboda mahaifinta ba shi da halin biyan wadanann kudade, a cewarta ma wannan kudin ma da ta kawo kayan dakinta aka sayar aka kawo.

Bayan da Alkalin kotun Mai Shari’a Aliyu Ibrahim Kani ya saurari jawabin wacce ake karar, ya bayar da umarnin a sakaya ta a kurkuku har zuwa lokacin da za ta kawo cikon kudin don fansar kanta.