✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za A Dauki Tsauraran Matakai A Kan Direbobin Manyan Motoci

Ana zargin direbobin tanka da haddasa hadurra a kan manyan hanoyoi.

A ’yan kwanakin nan an samu karuwa a rahotannin hadurran mota a kan hanyoyin Najeriya.

Wasu daga cikin hadurran kuma direbobin tanka ake zargi da haddasa su.

Mai yiwuwa wannan ne ya sa Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai a kan su.

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan matakan da ma zarge-zargen da ake yi cewa direbobin na tukin ganganci.