✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dauki Jose Peseiro sabon kocin Super Eagles

Jose Mourinho ne ya ba Hukumar NFF din ta dauka a matsayin mai horar da ‘yan wasanta.

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF, ta sanar da daukar Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Hukumar ta sanar da hakan bayan taronta na ranar Laraba.

A sanarwar, “bayan nazarin wasikar shugaban kwamitin tsare-tsare da ci gaban wannan hukumar, Kwamitin Zartarwa ya amince da zabar Mista Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.

“Sai dai hukumar ta amince kocin wucin gadin tawagar wato Austin Eguavoen ya jagoranci kasar a gasar Kofin Afirka da za a fafata a Kamaru, shi kuma sabon kocin ya zama mai lura a gasar. Hakan zai sa su fara samun alakar aiki tare tun yanzu.

Jose Santos Peseiro tsohon dan kwallo ne mai shekara 61 da ya buga tamaula a matsayin dan wasan gaba.

Ya taba horar da kungiyoyin Sporting CP ta Portugal da FC Porto da Real Madrid a matsayin mataimakin koci, da tawagar kwallon kafa ta Saudi Arabia, sannan a karshe-karshen ya horar da kasar Venezuela, inda suka rabu a watan Agustan da ya wuce.

Dan asalin kasar Portugal ne wanda kocin AS Roma, Jose Mourinho ya ba Hukumar NFF din ta dauka a matsayin mai horar da ‘yan wasanta, inda har wasu rahotanni suka nuna cewa Mourinho din ya yi alkawain zai rako shi Najeriya ranar da za a gabatar da shi.