Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta dakatar da kwamandanta na karamar hukumar Dala, Suyudi Hassan Muhammad.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ustaz Ibn Sina ne ya dakatar da Suyudi bisa zargin karkatar da kayan tallafin COVID-19.
- ASUU ta musanta janye yajin aiki
- An kama mutanen da ‘suka ci balangun gawar ‘Yan sanda’
- An kama mai abincin sayarwa da ke girki da ruwan wanke gawa
Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ibrahim Lawal Fagge ya fitar ce an dakatar da Suyudi Hassan ne na tsawon wata daya.
Hakan na zuwa ne bayan ranar Juma’a an tashi baram-baram a zaman neman maslaha da aka yi da wadanda suka yi korafin da wanda ake zargin da karkatar da kayan tallafin da aka ba su su raba wa jama’a.