✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage ziyarar da Pele zai kawo Najeriya

A ranar Litinin da ta wuce ne kamfanonin da suka shirya yadda shahararren dan kwallon duniya kuma haifaffen Brazil Pele zai kawo Najeriya suka bayar…

A ranar Litinin da ta wuce ne kamfanonin da suka shirya yadda shahararren dan kwallon duniya kuma haifaffen Brazil Pele zai kawo Najeriya suka bayar da sanarwar  dage wannan ziyara har sai wani lokaci.
A wata sanarwa da suka fitar inda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya samu kwafe, an nuna shahrarren dan kwallon ba zai samu damar kawo ziyara Najeriya ba ne saboda rashin lafiya.
An ce dan kwallon ya kamu da rashin lafiya ne a ranar Juma’ar da ta wuce watau 5 ga watan nan da muke ciki bayan an shirya zai fara ziyarar ce a ranar  11 zuwa 12 ga wannan wata da muke ciki.
“Muna ba magoya bayan tsohon dan kwallon hakuri a bisa wannan dagewar ziyarar tasa da muka yi saboda rashin lafiyarsa. Mun dage wannan ziyarar ce saboda bai dace mu ce lallai sai ya shigo Najeriya ba ganin ya kamu da rashin lafiya”.
Masu shirya ziyarar sun tabbatar za su mayar wa duk wadanda suka sayi tikitin shiga filin kwallon don yin ido biyu da Pele kudinsu ba tare da wata matsala ba.  Sai dai sun ce nan gaba kadan za su sanar da ranar da tsohon dan kwallon zai kawo ziyara Najeriya idan ya samu sauki.
An dai shirya zai kawo ziyarar ta kwana biyu ce daga jiya Alhamis zuwa yau Juma’a inda zai sauka a Legas.