Alkalin babbar kotun jihar Kaduna da ke zamanta a GRA Zariya, Mai Shari’a Kabir Dabo, ya dage yanke hukunci a kan wani wanda ake tuhuma da yin sanadiyyar mutuwar wata yarinya ‘yar shekara biyu da wata tara ta hanyar yi mata fyade.
Alkalin ya dage hukuncin ne har sai ranar 10 ga watan Yuni 2020.
Mai Shari’a Kabir Dabo ya dauki wannan matakin ne a lokacin da ya kammala karanta bayanai game da matsayin kotun a kan Usman Shehu Bashir, wadanda ke nuna cewa an samu wanda ake tuhuma da laifi.
“Akwai masu zaman jiran hukuncin kisa har 10,000 da ba a aiwatar masu da hukuncin da aka yanke masu ba tun kimanin shekara 15 da suka gabata”, inji Kabir Dabo.
A cewar alkalin, babu dalilin da kotuna za su yanke hukuncin kisa amma gwamnoni su ki aiwatarwa duk da kokawar da suke yi game da cunkoso a gidajen yari.
Mai Shari’ar, ya yi kira ga gwamnoni da su rika sauke nauyin da ke kansu ta fannin gudanarwa ko a sami raguwar cunkoso a gidajen yari.
Kusan shekara biyar ke nan ana wannan shari’a, kuma mutane da dama, musamman masu fafutukar kare hakkokin mata da kananan yara, za su zaku su ga hukuncin da za a yanke a kan wanda ake tuhuma.