Gwamnatin Jihar Filato ta dage dokar hana fita a jihar, daga ranar yau Alhamis zuwa ranar Lahadi mai zuwa.
Gwamnan Jihar Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga al’ummar Jihar, a gidajen rediyo da talabijin kan cikar wa’adin dokar hana fita na mako daya da ya sanya a jihar, a yammacin ranar Larabar nan.
A cewar Gwamnan, gwamnatin ta dage dokar ne domin ta bai wa jama’ar jihar dama su fita su sarara, su sami damar sayen kayayyakin abinci.
Daga daren ranar Lahadin kuma dokar za ta ci gaba da aiki, har ya zuwa ranar 23 ga watan Afrilu, kamar yadda jami’an kiwon lafiya, suka bayar da shawara.
- COVID-19: Yadda dokar hana fita ta yi aiki a Filato
- Za a hukunta duk wanda ya taka dokar hana fita a Filato
- Coronavirus: ‘Dalilin dakatar da komai a Filato’
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin ta jihar Filato, ta kafa dokar hana fita na wa’adin tsawon mako guda.
Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne don kaucewa bullar cutar coronavirus a jihar.