✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage Aguero daga yin wasanni hudu

Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta dage dan kwallon Manchester City Sergio Aguero daga yin wasanni hudu saboda laifin ketar da ya yi wa…

Hukumar shirya kwallon kafa ta Ingila ta dage dan kwallon Manchester City Sergio Aguero daga yin wasanni hudu saboda laifin ketar da ya yi wa dan kwallon Chelsea Dabid Luis a ranar Lahadin da ta gabata.

Manchester City ta sha kashi ne da ci 3-1 a gida a wasan da ta yi da kulob din Chelsea a ranar Lahadin da ta wuce kuma ana gab da tashi wasan ne sai Aguero ya yi wa Dabid Luis keta da hakan ta janyo hatsaniya a tsakanin ’yan kwallon biyu inda alkalin wasan ya ba shi jan kati (red card).
Yanzu dai Aguero ba zai buga wasan da kulob din City zai yi da na Leicester City da na Watford da na Arsenal da kuma na Hull City a gasar firimiyar Ingila ba.
Shi ma takwaransa Fernandhinho an dage shi daga yin wasanni uku saboda jan katin da ya samu bayan ya tunkude dan kwallon Chelsea Cesc Fabgregas a lokacin da hatsaniya ta kaure a tsakanin ’yan kwallon.
A watan Agustan da ya gabata ne aka taba dage Aguero daga yin wasa bayan ya yi wa dan kwallon West Ham United Wanton Reid keta.