Kotun tafi-da-gidanka kan tsaftar muhalli a jihar Kano ta ci tarar wasu kamfanoni N1m saboda karya dokar tsaftar muhalli ta wata-wata a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kamfanonin da lamarin ya shafa sun hada da Kamfanin Kera Tankuna na GP da kuma takwaransa na JP.
- Dalilin da Buhari ya gaza cika alkawuransa –Bashir Tofa
- Za a bayyana Gwarzon Shekara na Gasar Haddar Al-Kur’ani
Alkalin kotun, Mai Shari’a Auwal Yusuf Suleiman ne ya yanke musu hukuncin ranar Asabar yayin zagayen gani da idon da suka yi a unguwar masana’antu ta Sharada dake Kano.
Alkalin ya ce an sami kamfanonin biyu ne da karya dokar wacce ta tanadi rufe wuraren kasuwanci a kowacce Asabar din karshen wata daga karfe 7:00 zuwa 10:00 na safe.
Hakan a cewarsa ya kuma saba da tanade-tanaden sassa na 61 da na 104 na Dokokin Tsaftar Muhalli na Kasa.
Daga nan sai ya yankewa kowanne kamfani hukuncin biyan tarar N500,000.
Da yake tsokaci bayan yanke hukuncin, Kwamishinan Muhalli na jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce kamfanonin da aka yankewa hukuncin ba sa cikin wadanda aka kebance daga dokar.
Ya ce an kebance wasu kamfanoni ne daga shiga aikin la’akari da irin ayyukan da suke gudanarwa.
Kwamishinan ya kuma yabawa mutanen gari saboda irin hadin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin aikin ya sami nasara a kowanne lokaci.
Kotun ta kuma hukunta wasu matuka babura da wani mahayin doki da aka same su suma da karya dokar.
Wasu daga cikin unguwannin da kotun ta zagaya sun hada da Bata da ’Yankura da Sabon Gari da Dakata da ‘Yankaba da Kings Garden da Fagge da Mayanka da Titin IBB da na Obasanjo da dai sauransu.