Rundunar ’yan sanda ta gano wani gidan cin kasuwar jarirai da aka yi masa badda kama a matsayi gidan shan barasa da mata masu zaman kansu a garin Nnewi na Jihar Anambra.
Rundunar ta kuma samu nasarar ceto wasu masu hudu masu juna biyu da ake kirdadon haihuwarsu yayin da ta kai simame gidan mai suna Cool Joint Bar- ma’ana matattarar shan barasa mai sanyi.
- Dalilin sace-sacen dalibai a Arewacin Najeriya
- Messi ya sake kafa sabon tahiri a Barcelona da gasar La Liga
- Yadda Mata Ke Neman Kawo Karshen Kashe-Kashe a Zangon Kataf
A sanarwar da Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Haruna Mohammed ya fitar a ranar Talata, ya ce matar wacce ta mallaki gidan mai suna Gladys Nworie Ikegwuonu a yanzu ta bazama.
Kakakin ’yan sandan ya bayar da sunayen ’yan matan da aka ceto wadanda dukkaninsu ’yan asalin jihar Ebonyi da suka hada da Chisom Okoye ’yar shekara 19, Chinecherem Clement mai shekara 18, sai kuma Blessing Ogbonna mai shekara 19 da Blessing Njoku mai shekara 21.
Kazalika, Kakakin ’yan sandan ya ce an kama wasu mutane biyu da ke da alaka da gidan; Abuchi Ani mai shekara 32 da Emeka Ikegwuonu mai shekara 46 kuma ana ci gaba da neman Gladys domin gurfanar da ita a gaban shari’a.
Ya ce ababen zargin suna da hannu wajen kamo ’yan mata da gayyatar maza su yi musu ciki sannan a sayar da jariran da suka haifa kuma a ce su kara gaba.