✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke su za su tsere da Dala 890,000 daga Najeriya

Wasu ‘yan kasar Lebanon sun shiga hannu a lokacin da suke yunkurin fasakwaurin kudade daga Najeriya zuwa kasarsu. Hukumar hana fasa kwauri (NCS) shiyyar Fatakwal,…

Wasu ‘yan kasar Lebanon sun shiga hannu a lokacin da suke yunkurin fasakwaurin kudade daga Najeriya zuwa kasarsu.

Hukumar hana fasa kwauri (NCS) shiyyar Fatakwal, Jihar Ribas ta kama mutanen ta kuma damka su ga hukumar EFCC mai yaki da laifukan da suka danganci kudade da tattalin arziki.

Kwamandan NCS na shiyyar, Auwal Mohammed ya ce jami’ansa sun damke mutanen ne a yayin da suke binciken fasinjojin wani jirgi da ke hanyarsa ta zuwa kasar ta Lebanon.

A cewarsa, mutum na farko an same shi yana dauke da tsabar kudi Dala 670,000, na biyun kuma yana dauke da Dala 220,000, wanda jimilla ya kama Dala 890,000.

Ya ce sun kama ‘ya kasar Lebanon din ne bisa zargin yunkurin fitar da tsabar kudade zuwa kasashen ketare ta haramtacciyar hanya.

Kwamandan ya kuma ce akwai yiwuwar a mallaka wa gwamnati kudaden da zarar an kammala bincike.

Da ya ke karbar wadanda ake zargin, babban mai bincike na EFCC a shiyyar Fatakwal, Macauley Olayinka ya ce za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.