✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke na hannun daman hambararren Shugaban Pakistan

Ana zarginsa da furta wasu kalamai a kan tsohon Shugaban Kasar, Asif Ali Zardari

An kama Sheikh Rashid Ahmed, tsohon Ministan Cikin Gida  kuma na hannun daman hambararren Firan Ministan kasar Pakistan, Imran Khan.

An kama shi ne ranar Alhamis sa’o’i bayan da aka sako wani babban dan adawa da ke tsare.

Ahmed wanda ke jagorantar wata jam’iyyar da ke kawance da Imran Khan, ya bayyana a kotu a Islamabad inda aka tsare shi.

’Yan sanda sun ce an kama Ahmed ne bisa wasu kalamai da ake zargin ya furta a kan tsohon Shugaban Kasar, Asif Ali Zardari, inda ya zarge shi da kitsa shirin kashe Imran Khan da ya kasance jagoran Darikar Insat ta Pakistan.

Raja Inayat ur Rehman, mamba a jam’iyyar ‘Pakistan Peoples Party’, ya yi zargin wanda aka tsaren “Ya yi kokarin tunzura jama’a.”

Kasar Pakisantan dai na ci gaba da fuskantar matsaloli daban-daban da suka hada da tabarbarewa tsaro da tattalin arziki da sauransu.