Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, ta cafke wani direban da karen motarsa ta daukan kaya a Jihar Kebbi makare da buhu 115 na tabar wiwi mai nauyin tan 2.07.
Kwamandan Hukumar reshen Jihar, Mista Peter Odaudu ne ya inganta rahoton yayin zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin.
- Daliban jami’ar Abuja na zanga-zanga kan karin kudin makaranta
- Marayun Abuja sun kubuta daga hannun ’yan bindiga
- Dan shekara 52 ya shiga hannu kan laifin kwanciya da ’yarsa
Ya ce jami’an hukumar sun cafke ababen zargin biyu a ranar Lahadi a Karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi.
“Ababen zargin da muka kama da misalin karfe 5.30 na Yammacin ranar Lahadi sun debo hanya ne tun daga birnin Akure na jihar Ondo da zummar sauke kayan da suka dauko a Jihar Sakkwato.”
A cewarsa, “mutanen biyu sun bayyana cewa mamallakin kayan a birnin Shehu yake kuma basu da wani bayani a kansa face lambarsa ta wayar salula wanda za su kira idan sun isa domin shaida masu wurin da za su sauke masa hajarsa..”
Kwamandan ya bukaci al’umma da su rika fallasa duk wani lamari da suka gani mai nasaba da safarar miyagun kwayoyi.
Yayin amsa tambayoyin manema labarai, direban motar ya amsa sanayya a kan nau’in kayan da suka dauko inda yake rokon Allah Ya jibinci lamarinsu domin a saukaka musu hukunci.