✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke jagoran ‘yan adawar Ivory Coast

Jami’an tsaron kasar Ivory Coast sun tsare jagoran ‘yan adawan kasar kuma tsohon Firaminista, Pascal Affi N’Guessan. An tsare shi ne bayan ya nesanta kansa…

Jami’an tsaron kasar Ivory Coast sun tsare jagoran ‘yan adawan kasar kuma tsohon Firaminista, Pascal Affi N’Guessan.

An tsare shi ne bayan ya nesanta kansa da gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara wanda ya sake cin zabe a karo na uku, lamarin da ya kawo cece-ku-ce a fadin kasar.

Iyalai da magoya bayan jam’iyyar N’Guessan sun ce jami’an tsaro sun cafke shi ne ranar juma’a a kan hanyarsa ta zuwa mahaifarsa ta Bongouanou a gabar da ke tsakanin Ivory Coast da Ghana.

Sun ce an tsare shi ne tare da wasu jagororin jam’iyyarsa biyu, bayan sun yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar ranar 31 ga watan Octoba.

Hukumar zaben kasar ta bayyana Shugaba Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 94 cikin 100 na kuri’un da aka jefa.

Gwamnatin kasar ta matsa wa jagororin adawar da take zargi da alaka da ‘yan ta’adda da kisan kai da zagon kasa da yunkurin hambarar da sabuwar gwamnatin.

An kashe sama da mutum 40 a zanga-zangar adawa da nasarar Ouattara a zango na  uku da ya samu tun a watan Agusta.

Karo na biyu kenan da Ouattara, mai shekara 78, ya ke yin tazarce inda ya yi zango biyu a karkashin dokar kundin tsarin mulkin kasar ta 2010, sannan kuma ya sake neman damar jagorantar kasar a karo na uku karkashin dokar mulkin kasar da aka sabunta a 2016.