✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bukaci a tallafa wa al’ummar Musulmi na garin Awi

An bukaci al’ummar Musulmi su taimaka wa ’yan uwansu mazauna garin Awi, karamar Hukumar Akamkpa da ke Jihar Kurosriba domin su gina masallacin Juma’a. Tun…

An bukaci al’ummar Musulmi su taimaka wa ’yan uwansu mazauna garin Awi, karamar Hukumar Akamkpa da ke Jihar Kurosriba domin su gina masallacin Juma’a.

Tun farko, Musulmin ne suka yi tattali har suka sayi filin da za su gina masalacin a hannun ’yan asalin garin da sa bakin basarakensu. Ta haka ne a tsakaninsu suka kafa wata farfajiya da suke yin Sallolin farilla biyar ciki, har ma da ta Juma’a, kamar yadda Malam Abdullahi Muhammad, Limamin masallacin ya bukaci haka, a zantawarsa da Aminiya.

Ya ce babbar matsalarmu ita ce ta a taimaka mana mu gina masallacin da za mu rika yin salloli biyar da kuma gina masallacin Juma’a. “Yanzu kaxan daga cikin filin ne muka samu muka buga kwano, muke yin Sallar Juma’a, don haka muke kira ga al’ummar Musulmi ko’ina a faxin Najeriya, a taimaka mana nan ba da jimawa ba ne ma muke son aza harsashin gina masallacin,” inji shi.

Da yake tsokaci game da ’yan asalin jihar da na karamar hukuma, limamin ya bayyana cewa ana samun masu shiga Musulunci to amma matsalar ta ilmantar da su  da kuma aikin yi ko sana’a.  “A nan ma akwai bukatar a rika taimaka musu domin idan har sun karbi Musuluncin nan ana korarsu daga gidajen iyayen su.”

Ya ci gaba da cewa “akwai bukatar a taimaka mana da kayan karatu da kuma rika tura su Arewacin Najeriya suna koyon karatun addinin Musulunci cikin harshen Ingilishi.”

Malam Abubakar har wayau ya bayyana cewa duk da cewa su tsiraru ne a garin na Awi, akwa bukatar ’yan uwa Musulmi masu hannu da shuni su taimaka masu domin wasun lokutan ma suna samun matsala wajen gudanar da harkokin addini, misali idan aka ce an samu rasuwa, wani ya mutu. Ya yi fatan ’yan uwa Musulmi za su taimaka wa al’ummar Musulmin Awi.