Ranar Juma’a 15 ga watan Mayu ake bude Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust karo na farko.
Gasar, wadda kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya zai gudanar da hadin gwiwar Gandun Kalmomi da Open Arts da suke Kaduna, ana sa ran ta kasance wata kafa ta bunkasa rubuce-rubucen adabi cikin harshen Hausa wadda za a rika gabatarwa duk shekara.
Wata sanarwa daga jagoran gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ta ce gasar za ta rika zuwa da maudu’in da ake so masu shiga su gabatar a cikin labaransu.
Maudu’in gasar
Maudu’in gasar ta bana shi ne “Matsalolin Mulkin Dimokuradiyya da Dambarwar Siyasa a Najeriya”.
“Dole masu shiga gasar su tunkari wannan batu a cikin labarinsu ta fuskar da suka ga dama, sai dai ana son labarin ya kasance kagagge, ba abin da ya faru a zahiri ba, ko a fassaro shi daga wani harshe ko wani rubutu na daban”, inji sanarwar.
Ta kara da cewa kowane labari kada ya gaza kalmomi 1,000, kada kuma ya wuce 1,500, kuma a kayata shi da ka’idojin rubutun Hausa da salo mai burgewa, a kuma kauce wa jefa batsa ko kalamai masu iya ta da hayaniya ko tashin hankali.
Wadanda suka cancanci shiga
“An shirya gasar ce domin matasa maza da mata masu shekara 18 zuwa 35 daga ko’ina a duniya, sannan suna iya shiga a daidaikunsu ko su hada hannu su biyu maza ko mata ko mace da namiji.
“Za a buga gajerun labaran da suka yi zarra daga na 1 zuwa a 15 a matsayin littafi don adanawa da kuma sayarwa da rarrabawa domin amfanin al’umma,” inji sanarwar.
Masu son shiga gasar za su aika da gajeren labarinsu zuwa: [email protected] tare da cikakken suna da takaitaccen bayanin mai shiga gasar da jawabi game da gajeren labarin da adireshin gida ko ofis da na imel da lambar waya.
Za a rufe gasar da karfe 12:00 na dare ranar 15 ga Yuli, 2020, kuma wadanda suka zo na daya zuwa na uku za su samu kyautar Naira 250,000 da Naira 150,000 da Naira 100,000 a wani bikin karramawa da za a yi a watan Disamban bana a Kaduna.