✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude gasar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC ta bana

A ranar Asabar da ta gabata ce kafar watsa labaran BBC ta fara gudanar da gasar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC ta bana. Gasar…

A ranar Asabar da ta gabata ce kafar watsa labaran BBC ta fara gudanar da gasar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC ta bana.

Gasar wacce ake gudanar da ita duk shekara, an fara ta bana ne tun daga ranar 17 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamban wannan shekara (2018).

Ana sa ran masoya kwallon kafa ne za su zabi dan kwallon da ya fi dacewa wajen lashe wannan gasa wajen kada kuri’arsu a kafar watsa labaran BBC ta yanar gizo.

Masana harkar kwallon kafa ne suka zabo ’yan kwallo biyar da za su fafata a wannan gasa da suka hada da: Medhi Benatia dan asalin Maroko da ke buga wa kulob din Jubentus na Italiya wasa, sai Kalidou Koulibaly dan Senegal da ke yi wa kulob din Napoli na Italiya kwallo sai Sadio Mane dan asalin Senegal da ke yi wa kulob din Liberpool wasa sai Mohammed Salah dan asalin Masar da ke bugawa kulob din Liberpool kwallo sai Thomas Partey dan asalin Ghana da ke bugawa kulob din Atletico Madrid na Sifen wasa.

A ranar 14 ga watan Disamba, 2018 ne BBC zai sanar da wanda ya lashe gasar da misalin karfe hudu da rabi na yamma agogon Najeriya.

’Yan kwallon da suka taba lashe wannan gasa a baya sun hada da Jay-Jay Okocha dan asalin Najeriya da Micheal Essien dan asalin Ghana da Didier Drogba da Yaya Toure ’yan asalin Kwaddebuwa da kuma Riyad Mahrez dan asalin Aljeriya.