✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude filin wasan motsa jiki na ‘yan sanda a Jihar Oyo

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo, Abiodun Odude ya kaddamar da sabon filin wasan kwallon Badminton da aka bude domin nishadantar da jami’an ’yan sanda. Filin…

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo, Abiodun Odude ya kaddamar da sabon filin wasan kwallon Badminton da aka bude domin nishadantar da jami’an ’yan sanda.

Filin wasan da aka gina a hedkwatar ’yan sanda ta Eleyele a Ibadan an rada masa sunan Kwamishinan ’yan sanda Abiodun Odude. Cikin jawabinsa a wajen bikin da ya samu halartar manya da kananan jami’an ’yan sanda, Kwamishinan wanda shi ne ya yanke kyallen tabbatar da bude filin wasan ya nuna matukar farin ciki da girmamawar da aka yi masa a cikin tarihin wasannin ’yan sanda a Jihar Oyo. Ya yi alkawarin a zamaninsa zai farfado da dukkan harkokin wasannin motsa jiki na jami’an ’yan sanda domin nishadantarwa bayan gudanar da ayyukan tsaron lafiyar al’umma a Jihar.

Da yake jawabi ga mahalarta bikin, Shugaban kwamitin samar da wannan filin wasa, Mataimakin Kwamishinan ’yan sanda D.C Attahiru Isa ya ce kwamitinsa ya fara tunanin samar da filin wasan ne a cikin watanni kadan da suka gabata a inda mafarkinsa ya tabbata bayan samun goyon bayan Kwamishinan ’yan sanda Abiodun Odude. Ya ce, goyon bayan da suka samu daga Kwamishinan ne ya karfafa masu gwiwar kai wa ga cimma wannan nasara. “Shi ne dalilin da ya sa muka rada wa filin wasan sunan Kwamishinan.”

DC Attahiru Isa ya ce, kwamitin ya yi nasarar kammala aikin gina filin wasan ne daga gudunmawar kudi da kayan aiki da ya samu daga kungiyoyi daban -daban har da manya da kananan ’yan sanda da suka bayar da tallafi domin cimma wannan buri.

Bayan bude filin wasan ne aka fara yin wasan kwallon Badminton a tsakanin CP Abiodun Odude da Mataimakinsa DC Sanusi Buba a inda Kwamishinan ya yi nasara da cin kwallaye 2 ba ko daya.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Oyo Adekunle Ajisebutu yana daga cikin wakilan ’yan sanda 6 da suka gudanar da wannan aiki.