Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce zuwa ranar Juma’a 24 ga watan Yuli 2020 an bude filayen jiragen sama guda 14 aka a fadin Najeriya.
An sake bude jigilar jiragen fasinjojin na cikin gidan ne bayan rufe su watan Maris da nufin takaita yaduwar cutar coronavirus
A ranar 8 ga watan Yuli ne Gwamnatin Tarayya ta fara da bude filayen jirage da ke Abuja da Legas. Sannan a ranar 11 ga watan ta bude na Kano da Maiduguri da Fatakwal da kuma Imo.
Budewar na zuwa ne bayan Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta tantance tabbacin daukar matakan kariyan cutar a filayen.
Tantancewanr na kan mayar da hankali ne wajen tabbatar da bayar da tazara da sauran matakan kare lafiya da kuma hana cutar yaduwa a tsakanin mutane.
A ranar 13 ga watan Yuli Darekta Janar na NCAA, Musa Nuhu ya ce sai bayan kimanin mako guda za a sake bude wasu filayen jirgin.
Zuwa yanzu dai filayen jirgi 14 ne aka bude da kasar bayan bude wasu karin guda shida da suka hada da na Victor Attah a Jihar Akwa Ibom; da na Kaduna da na Yola da kuma na Kalaba.
Sauran su ne na Sultan Abubakar, Sokoto; da na Birnin Kebbi da na Jos da kuma na Benin a jihar Edo.