✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An biya ’yan kwallon Najeriya alawus din da suke bi bashi

Tawagar ’yan kwallon Najeriya (U-23) su kimanin 29 ne Ma’aikatar matasa da wasanni karkashin shugabancin Barista Solomon Dalung ta biya alawus din da suke bin…

Tawagar ’yan kwallon Najeriya (U-23) su kimanin 29 ne Ma’aikatar matasa da wasanni karkashin shugabancin Barista Solomon Dalung ta biya alawus din da suke bin ta bashi na kwanaki 10.
Rahoton ya nuna an biya kowane dan kwallo Dala dubu 1 da 650 kwatankwacin Naira dubu 676 da 500 a matsayin kudin alawus dinsu na tsawon kwanaki 11 da suka yi a sansanin horar da su a Amurka kafin a fara gasar Olamfik.
An shirya ba ’yan kwallon alawus din Dala 150 ne a kullum a tsawon lokacin da za su kwashe suna samun horo a Amurka, kwatankwacin Naira dubu 61 da 500 a kowace rana.
Ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ne ya bayar da umarnin biyan ’yan kwallon a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ya gana da su jim kadan bayan kungiyar ta doke Sweden da ci 1-0 a wasa na biyu da hakan ya ba kungiyar damar hayewar matakin kwata-fainal a bangaren kwallon kafa na maza a gasar Olamfik da ke gudana a Brazil.
Idan za a tuna, kafin wannan lokaci ’yan kwallon sun koka ne akan rashin ba su kyakkyawar kula a Amurka da hakan ya jefa su cikin mawuyacin hali, ganin yadda suke ba marada kunya duk da halin da suke ciki ne ta sa Ministan ya kai musu dauki.