✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bayyana ’yan kwallon da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon Duniya

Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) a ranar Litinin da ta wuce ne ta bayyana sunayen ’yan kwallo 23 da ake ganin za su…

Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) a ranar Litinin da ta wuce ne ta bayyana sunayen ’yan kwallo 23 da ake ganin za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon Duniya. Sai dai za a sake zaftare 20 daga cikin wannan adadi ya zamo ’yan kwallo uku ne kacal za su fafafata a gasar a watan Janairun 2016. Sannan daga cikin wadannan sunaye da hukumar FIFA ta fitar biyu ne suka fi daukar hankali watau na Cristiano Ronaldo da kuma na Lionel Messi. Kimanin shekara bakwai kenan wadannan ’yan kwallo suke lashe gasar a tsakaninsu.

Tun da farko dai Hukumar ta samar da sunayen ’yan kwallo 53 ne kafin ta zaftare su zuwa 23 sannan haka za a cigaba da zaftarewa har su koma uku kafin watan Janairun badi, inda uku ne kacal za su fafafata a tsakaninsu. Wanda ya fi samun kuri’a ne dai yake zama Gwarzon dan kwallon duniya (Ballon D’Or).
Masu horarwa a kasashen duniya da kyaftin-kyaftin da kuma wadansu gidajen jaridu ne a sassan duniya suke kada kuri’a wajen zakulo Gwarzon dan kwallon Duniya a kowace shekara. Sannan ana sa ran za a fara kada kuri’a ce daga ranar 26 ga watan nan da muke ciki zuwa 20 ga Nuwamban 2015 kafin a rufe sai dai ba za a bayyana wanda ya lashe ba sai a bikin da Hukumar za ta shirya a hedkwatarta da ke Zurich na Suwizilan a watan Janairun 2016.
Idan za a tuna Cristiano Ronaldo ne yake rike da kambun a halin yanzu bayan ya lashe sau biyu a jere. Haka kuma Lionel Messi ne ya kafa tarihin dan kwallon da ya lashe gasar har sau hudu a jere.
Sunayen ’yan kwallo 23 da FIFA ta fitar sun hada da 11 daga gasar La-Liga ta Sifen da kuma 5 daga gasar firimiya ta Ingila da 5 daga gasar rukunin Jamus (Bundesliga) yayin da gasar rukunin Faransa (Ligue 1) take da daya kamar yadda gasar Serie A ta Italiya ita ma aka zakulo dan kwallo daya.
’Yan kwallon sun hada da Sergio Aguerro (Manchester City) sai Gareth Bale (Real Madrid) sai Karim Benzema (Real Madrid) sai Cristiano Ronaldo (Real Madrid) sai Kebin De Brune (Manchester City) sai Eden Hazard (Chelsea) sai Zlatan Ibrahimobic (PSG) sai Andres Iniesta (FC Barcelona) sai Toni Kroos (Real Madrid) sai Robert Lewandoswski (Bayern Munich) sai Jabier Mascherano (FC Barcelona) sai Lionel Messi (FC Barcelona).
Sauran sun hada da Thomas Muller (Bayern Munich) sai Manuel Nuer (Bayerrn Munich) sai Neymar (FC Barcelona) sai Paul Pogba (Jubentus) sai Iban Rakitic (FC Barcelona) sai Arjen Robben (Bayern Munich) sai James Rodriguez (Real Madrid) sai Aledis Sanchez (Arsenal) sai Luis Suarez (FC Barcelona) sai Yaya Toure (Manchester City) da kumaArturo bidal (Munich).