A Yammacin yau na Juma’a ne aka sanar da Maryam Umar a matsayin gwarzuwar gasar gajerun kagaggun labarai ta mata zalla wato Hikayata ta 2020 a yayin bikin karrama gwarazan da BBC Hausa ta shirya a Abuja.
Labarin “Rai da Cuta” wanda Maryam Umar mai shekara 20 ta rubuta shi ne ya zama zakara a gasar ta shekara-shekara.
Bayan tantance fiye da kagaggun labarai 400 da mata daban-daban suka rubuta, alkalan na BBC Hausa sun fitar da uku da suka yi wa sauran fintinkau.
A tattaunawar da Aminiya ta yi da gwarazan matan uku da suka yi zarra a gasar Hikiyata ta bana, sun bayyana farin cikinsu matuka a yayin da kowace daya daga cikinsu ta ambaci cewa burinta na isar da sako da kuma haskakawarta a idon al’umma sun cika.
Labarin “Rai da Cuta”
Maryam Umar ta lashe gasar a bana, ta rubuta labarinta ne a kan Azima, wadda mijinta ya dawo daga tafiya tare da alamar cutar COVID-19 a tare da shi.
Duk da cewa matarsa na da tsohon ciki, ya ki killace kansa sannan ya ki yarda cewa alamar cutar ce a tare da shi.
Ganin haka ne Azima ta kulle shi a daki, amma ba a jima ba ta gano cewa mijin nata ya riga ya harbue ta da COVID-19.
Kamuwarta da cuta ya yi sanadiyyar abun da ke cikinta, ita ma ta shiga fadi-tashin tsira da ranta.
Marubuciyar labarin dalibai ce a Tsangayar Aikin Lauya ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Maryam Umar ce gwarzuwar gasar BBC Hausa ta gajerun kagaggun labarai ta mata zalla, Hikayata ta 2020.
Labarin da ya zo a matsayi na biyu a gasar wanda bana shi ne karo biyar na gasar, shi ne labarin “Numfashin Siyasata” wanda Surayya Zakari Yahaya ta rubuta.
Labarin na uku kuma shi ne wanda Rufaida Umar Ibrahim ta rubuta mai suna “Farar Kafa”.
Labarin “Numfashin Siyasata”
“Numfashin Siyasata” labarin wata matashiya ce da ta shiga harkar siyasa daa zimmar share wa al’ummarta hawaye saboda rashin cigaba da ke addabar su.
Amma kuma al’ummar da take neman ta kawo wa sauki suka juya mata baya, kawai saboda kasancewarta mace.
Saboda jajircewarta wajen neman kowa wa al’ummarta cigaba ya saka aka aka hallaka mahifanta; ita ma an yi yunkurin kashe ta amma ta tsallake rijiya da baya.
Labarin “Farar Kafa”
Labari ne a kan wata baiwar Allah mai suna Ramatu.
Wannan labari ne kan yadda illar yarda da camfi ya jefa Ramatu a cikin mawuyacin hali.
Bayan aurenta mijinta yai ta gamuwa da jarrabawa iri-iri kuma ya camfa cewa tana da farar kafa shi ya sa wadannan iftila’i ke fada wa kansa.
Rahama ta sha tsangwama dalilin haka kuma aka yi mata lakabi da mai farar kafa.