✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An bankawa ofishin INEC wuta na jihar Imo

A safiyar yau Litinin wasu sun bankawa ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC wuta da ke garin Orlu a jihar Imo. Wutar…

A safiyar yau Litinin wasu sun bankawa ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC wuta da ke garin Orlu a jihar Imo.

Wutar ta fara lakume ginin ofishin ne da safiyar yau tare da wasu bangaren ginin harabar ofishin.

Ana fargabar faruwar hakan ne sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a mazabun Orlu/Orsu/Oru ta Gabas da ke jihar.

An dai samu rikicin zabe a mazabun, inda aka yi zaben a rumfuna 18 da ke mazabar Orlu, hudu daga cikin rumfunan zabe 18, an yi su ne a hedkwatar INEC da ke Owerri babban birnin jihar sakamakon wasu ‘yan bangar siyasa da suka nufi harabar don tada rikici ranar Asabar 25 ga Janairun 2020.