✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ba masallatai da coci-coci wa’adin mako 2 su sauke lasifikoki a Ibadan

Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da wa’adin mako 2 ga dukkan masallatai da coci-coci da kulob-kulob da wuraren shakatawa da shagunan sayar da kaset da…

Gwamnatin Jihar Oyo ta bayar da wa’adin mako 2 ga dukkan masallatai da coci-coci da kulob-kulob da wuraren shakatawa da shagunan sayar da kaset da bidiyo da garmaho da motoci masu yawon kade-kade da bushe-bushe a cikin jama’a domin tallar hajarsu da su daina yin amfani da na’urar kara sauti a cikin wannan lokaci ko su fuskanci hukunci.

A makon jiya ne gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe wasu coci uku a Ibadan saboda yawan karar sauti da ke fitowa daga cikinsu, wanda yake zama takurawa ga jama’a.

Wasu mutane mabiya addinan Musulunci da Kiristanci da Aminiya ta jiyo ra’ayinsu dangane da wannan wa’adi, sun nuna cewa dokar ta yi daidai sai dai akwai bukatar karin wa’adi da za a wayar da kan jama’a game da amfanin kafa dokar ga jama’a. 

Da yake bayar da wannan wa’adi a wajen taro da ’yan jarida a ranar Talata da ta gabata a Ibadan, Kwamishinan Muhalli Da Albarkatun Ruwa, Cif Isaac Ishola, ya yi bayanin cewa, kafin gwamnati ta dauki wannan mataki sai da ta yi taruka a lokuta daban-daban da dukkan masu ruwa da tsaki daga bangaren addinai da suka hada da kungiyoyin Kiristoci na (CAN) da (PFN) da kungiyar limamai da malaman Musulunci da aka nemi hadin kansu a game da sabuwar dokar.

Kwamishinan ya ce, dokar tsaftace muhalli a jihar ta amince da iyakar nisan 90db (Decibel) mita 2.5 a yankin masana’atu a yayin da aka amince da nisan 60db da 45db na karar sauti na rana da dare ga mazauna unguwanni. Ya ce dukkan karar sautin da ya wuce wanda doka ta amince, ya zama hayaniya da takura wa jama’a da zai zama illa ga lafiyarsu.

Ya ce, daga yanzu dukkan wanda aka samu da taka wannan doka bayan cikar wa’adin mako 2, to za a rufe irin wadannan wurare ba tare da bata lokaci ba. Kuma wadanda suka mallaki irin wadannan wurare wajibi ne su kulla yarjejeniya da sanya hannu kafin gwamnati ta amince da sake bude masu wuraren.

Cif Isaac Ishola ya ce gwamnati ta tanadi dakaru 100 na rundunar Yes-O da kotun tafi da gidanka guda 2 da za su rika lura da gurbatattun wurare da dagwalon shara daga masana’antu da kamfanoni da za a rika hukunta su a duk lokacin da aka kama su. Dakarun za su fara yin sintiri domin kama masu zubar da shara barkatai da masu saye da sayarwa a kan hanyoyi da mabarata domin tsaftace muhalli.

Da yake karin bayani a kan ayyukan rundunar, Kwamishinan ya ce kimanin mutane 400 aka kama da laifin saye da sayarwa a kan hanya da mutane 250 da laifin zubar da shara barkatai da gonakin kiwon kaji guda 2 da dabbobi guda 4 masu yawon kiwo a kan hanya da gonar kiwon Alade guda 1 tare da kasuwar katako ta Temidire, wadanda dokar ta fada kansu aka rufe dukkansu.