Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta ba wa maniyyata aikin Hajjin 2022 wa’adin kwana bakwai su tabbata sun kammala biyan kudin kujera.
Hukumar ta kuma sanar cewa ranar 12 ga watan Mayu, 2022 za ta rufe karbar kudin kujera daga maniyyatanta.
- An kama shi yana sayar da garin katako a matsayin maganin gargajiya
- 2023: APC ta tsawaita lokacin sayar da fom din takara
Da yake yi wa ’yan jarida jawabi ranar Alhamis, Babban Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Danbatta, ya ce duk maniyyacin da bai cika kudin kujerarsa ba har wa’adin ya cika to sai dai ya jira wata shekarar.
“Hukumar na da maniyyata akalla 2,500 da suka yi zubin kudin aikin Hajji, kuma wadanda suka fara ajiye kudadensu hukumar za ta fi ba wa muhimmannci wajen wajen rabon kujearu”, inji shi.
Ya kuma bukaci maniyyata da suka haura shekara 65 a duniya da su je su karbi kudadensu, saboda gwamnatin Saudiyya ta haramta musu shiga kasar domin halartar aikin Hajji a bana.
Idan ba a manta ba, Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta ayyana Naira miliyan N2.5 a matsayin kudin kujerar aikin Hajjin 2022 na wucin gadi, kafin kammala lissafi a fitar da ainin abin da maniyyatan kowace jiha za su biya.
An dai dora laifin tashin gwauron zabon kujerar aikin Hajji a kan tashin Dala da karin harji daga gwamnatin Saudiyya da kamfanonin jirgin sama.