✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ba makiyaya kwana 7 su bar dazukan Jihar Ondo

'Duk mai son yin kiwo ya tabbata ya yi rajista nan da kwana bakwai'

Gwamnan Jihar Ondo ya ba wa makiyaya wa’adin kwana bakwai su tattara su fice daga daukacin dazukan jihar.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar, ya kuma haramta yin kiwo da dare a fadin jihar nan take, da kuma kora dabbobi ta manyan tituna ko ba wa kananan yara kiwon su.

“Domin nuna karamci, gwamnatinmu ta ba da kwana bakwai (daga Litinin 18 ga Janairu 2021), ga duk masu son ci gaba da sana’ar kiwo a jihar da ya je ya  yi rajista da hukumomin da suka dace,” inji sanarwar da ya fitar.

Akeredole, ya ce yin hakan ya zama wajibi, kasancear yawancin barnar da ake yi a cikin gonaki na aukuwa ne a cikin dare.

Matakin, a cewarsa shi ne abin da ya dace Gwamnatin Jihar Ondo ta dauka domin kawo karshen ayyukan bata-gari masu fakewa a matsayin makiyaya suna garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa bata-garin na boye mutanen da suka yi garkwa da su ne a cikin dazukan, suke kuma tsara karbar kudin fansa.

Gwamnan wanda ya bayyana damuwa game yawaitan ayyukan masu garkuwa da mutane a jihar ya ce wajibinsa na ya dauki matakan da suka dace domin kare rayuwan al’ummar jihar da yake mulka.

%d bloggers like this: