✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta rage wa’adin bizar daliban kasashen waje

Gwamnatin Shugaban Trump na shirin rage wa’adin bizar dalibai ’yan kasashen waje da ke karatu a kasar

Gwamnatin Amurka na shirin rage wa’adin shekarun biza da ake bai wa daliban kasashen waje masu zuwa kasar karatu zuwa shekara hudu.

A bukatar da Ministan Tsaron Cikin Gida ya nema, Ma’aikatar Harkokin Waje ta nemi a rage wa’adin bizar daliban da suka fito daga kasashen da ake goyon bayan ta’addanci zuwa shekara biyu.

Dangane da dokar, yanzu daliban da ke zuwa karatu a Amurka za su iya zama a kasar har sai sun kammala karatunsu.

Idan aka tabbatar da rage wa’adin bizar, dalibai ’yan kasashen waje za su rika neman karin wa’adi ne idan ba su kammala karatunsu cikin shekara hudu ba, ko kuma suna da rashin lafiya ko kuma in sun samu wani dalili mai karfi na zama a kasar.

Bisa sabon tsarin, za a rika bai wa dalibai biza ne a rukunan  ‘F’ da ‘J’ da kuma ‘I.’