✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta fara hawa teburin tattaunawa da ’yan Taliban

Tattaunawar dai ita ce irinta ta farko tun bayan janyewar Amurka daga Afghanistan.

Manyan jami’an gwamnatin Taliban da wakilan gwamnatin Amurka sun hau teburin tattaunawa don bude sabon shafi a dangantakarsu a kasar Qatar.

Mai rikon mukamin Ministan Harkokin Wajen Afghanistan, Mullah Amir Khan Muttaqi, ya tabbatar ranar Asabar.

Tattaunawar ta ido da ido, wacce aka fara a birnin Doha ranar Asabar, ita ce irinta ta farko tun bayan janyewar dakarun Amurka daga Afghanistan a watan Agusta, lamarin da ya kawo karshen mamayarsu ta shekara 20.

A cewar Ministan, babban abin da wakilan kasarsu suka fi mayar da hankali a tattaunawar shi ne yadda za a samar da agaji ga mutane, yana mai cewa sanya hannu a kan yarjejeniyar da Taliban ta cimma da Amurka a birnin Washington a bara ne ya share fagen janyewarta daga Afghanistan.

Ministan ya kuma ce sun bukaci Amurkan ta dage takunkumin da ta kakaba wa asusun Babban Bankin kasar da ke ketare.

Kazalika, Mullah Amir ya kuma ce kasar ta yi alkawarin tallafa wa mutanen Afghanistan da rigakafin cutar COVID-19 kyauta.

Daga bisani kuma, tawagar ta Taliban zata tattauna da wakilan Tarayyar Turai (EU).

Sai dai a ranar Juma’a, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce tattaunawar ba ta da alaka da amincewa da gwamnatin Taliban a hukumance, sai don ci gaba da tattauna manufofin kasar ta Amurka a can.

Kazalika, Ma’aikatar ba ta bayyana sunan jami’in gwamnatin da zai je birnin na Doha ba domin tattaunawar daga bangaren Amurka.