✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta dakatar da bai wa Nijar tallafi

Za a ci gaba da taimakon agajin jin kai na ceton rai da abinci.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da dakatar da wasu shirye-shirye da su kunshi ba da agaji ga Nijar bayan hambarar da zababben shugaban kasar da majalisar soji ta yi.

A karshen makon da ya gabata ne Faransa ta dakatar da duk wani taimakon raya kasa da take bai wa Nijar bayan juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum.

Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashe da dama ma sun dakatar da goyon bayansu.

Duk da haka, “za a ci gaba da taimakon agajin jin kai na ceton rai da abinci” kuma Amurka za ta ci gaba da gudanar da ayyukan diflomasiyya da tsaro don kare jami’anta a kasar, in ji shi.

Nijar na samun kusan dala biliyan biyu a duk shekara a matsayin taimakon raya kasa a hukumance, a cewar Bankin Duniya.