✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Na fara awon juna biyu a asibiti amma har yau ba a mini allurar riga-kafin sarke-hakora ta tatanas ba ga shin a kai watanni bakwai,…

Na fara awon juna biyu a asibiti amma har yau ba a mini allurar riga-kafin sarke-hakora ta tatanas ba ga shin a kai watanni bakwai, ko sun manta ne? Zan iya yi yanzu ko lokacinta ya kure? Sau nawa ya kamata a yi wannan allura kafin a haihu?

Daga Maman Sayyed

Amsa: Allurar kariya daga Tatanas wadda ake wa mace mai juna biyu ana yinta ne domin kare abinda ciki daga ciwon sarke-hakora. Ba dole bane a miki a kowane ciki da kika samu in dai a juna biyun da suka wuce an miki domin allurar takan kai shekaru 5-10 a jikinki tana aikin samar da kariya. Don haka a cikin fari ne ya zama wajibi a yi a kalla sau biyu, a ciki na biyu wasu sukan iya cewa a kara sau daya, amma a ciki na uku in dai ba dogon hutun haihuwa mace ta samu ba da ya wuce shekaru biyar (tsarin iyalin shekaru biyar zuwa sama) ba dole bane.

Wai shin al’adar mata na canzawa ne lokaci-lokaci? Domin mai dakina da kwanaki uku-uku take yanzu kuma biyar ne zuwa shida.

Daga Abban Ummulkhair

Amsa: E, al’ada za ta iya canzawa daga kwanaki uku zuwa biyar zuwa bakwai ma, dangane da yanayin halin da mace ta samu kanta a ciki na ciwo ko na jin dadi ko na damuwa ko na matsi kamar matsin tafiya ko na karatu misali, ko sanadiyar wasu magunguna kamar na tsarin iyali ko ma na wani ciwo na daban.

Mai ciwon kanjamau zai iya auren wadda ba ta da ciwon domin mukan ji ana cewa idan mutum na shan maganin rage kaifin ciwon ba zai sa wa matarsa ba.

Daga Salihu A., Lagos

Amsa:  A’a bamu cika son mai dauke da kwayar cutar kanjamau ya auri maras ciwon ba, domin a ko da yaushe akwai hadarin kamuwa ko da kuwa mutum na shan magungunan rage kaifin ciwon. Tabbas an tabbatar kwayoyin na rage hadarin kamuwa ga ma’aurata wadanda dayansu ba dauke da ciwon amma kariyar ba dari bisa dari bace.

Nine na mari wani yaro sai na ga yana habo. Duk da dai jinin ya tsaya ko habon na da alaka da marin?

Daga Ibrahim, Kaduna

Amsa: E, da alama zubar jinin na da alaka da marin domin mari mai karfi zai iya fasa wata magudanar jini a hanci musamman a yara, don haka wasu lokuta sai an kai zuciya nesa dangane da irin bugun da za a yi wa yara wadanda jikinsu bai yi kwari ba sosai. A irin wannan yanayi da an ga habon sai a yi sauri a samu auduga mai tsabta a tura kadan a bakin kofar hancin da ke zubar da jinin (kada a rufe duka kofofin hancin biyu) a daga kan yaron sama. Bayan kamar minti biyar sai a cire, za a ga jini ya tsaya. Idan bai tsaya ba a kara sa wata audugar a garzaya asibiti.