✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban kan lafiya

Wai da gaske dusar masara, dawa, alkama, da dangoginsu na da amfani ga jikin dan Adam? Daga Nasir Kainuwa, Hadejia Amsa: kwarai kuwa, duk da…

Wai da gaske dusar masara, dawa, alkama, da dangoginsu na da amfani ga jikin dan Adam?

Daga Nasir Kainuwa, Hadejia

Amsa: kwarai kuwa, duk da cewa wani bangare na dusar hatsi jiki ba ya tsotse ta, tana da amfani sosai, domin tana wanke babban hanji ta kuma hana taurin bayan gida da kiyaye aukuwar ciwon daji na babban hanjin. Ba dusar hatsi kawai ba, har tukar abinci irinsu aya da goruba wadda idan mun tsotse zakin muke furzarwa, duka suna da amfani, don haka furzarwar ba daidai ba ne. Ka san akwai ma wadanda sukan tattara irin wannan dusa da tuka su tura wa dabbobi, ba su san amfanin suke ba wa dabbobin ba.

Sauran bangaren da jiki ke iya tsotsa yana da amfani wajen tsane dattin jini na antiodidants da maikon jini irinsu cholesterol.

Ko akwai magungunan rage kwadayin abinci a likitance?

Daga Abdullahi Jalingo

Amsa: E, kwarai kuwa akwai. Sai dai maganin an ma daina amfani da shi saboda matsalolin da yake kawowa sun fi amfaninsa yawa. Sa’annan akwai magunguna na wasu abubuwa daban wadanda matsalolinsu shi ne rage sha’awa ko kwadayin abinci. Misali, ai da yawan magungunan ciwon suga ma suna iya rage sha’awar cin abinci. Amma ka ga ai ba ka sha maganin ciwon suga ba alhali ba ciwon ne da kai ba.

Wai tsakanin dankalin gida wato dankalin Hausa da na Turawa wane ne ya fi amfani ga jiki?

Daga Ahamad A.K

Amsa: Ai dukansu suna da amfani a jiki domin suna da sindarin abinci na carbohydrate mai kara kuzari da sinadaran bitaman da na ma’adinai. Sai dai dankalinmu na gida wato dankalin Hausa ya nunka na Turawa a irin wadannan sinadarai na bitaman da ma’adinai. Misali akwai bitaman na rukunin A da babu ma a na Turawa, ga bitaman na rukunin B6 da ma’adinin potassium da magnesium da suka fi yawa a namu na Hausa. Ka san ai mutane idan aka ce wannan abinci na Turai ne sai su fi ba shi muhimmanci a kan namu na gida. Tabbas babu ko tantama dankalin gida ya fi na Turawa amfani a jiki, sai dai da yake ya fi na turawa tauri zai iya ba wa wasu matsalar kumburin ciki, akasin na Turawa da bai cika sa kumburin ciki ba.

Ko tauna cingam yana da wata fa’ida?

Daga Ahmad Bichi

Amsa: E, ai ko ba komai akan motsa muka-muki. Sa’annan cingam mai sinadarin menthol yana iya sa baki kamshi na dan wani lokaci. Sai dai an fi son maras sukari, domin idan aka tauna mai suga zai iya makalewa a kan hakora, kwayoyin cuta su zo su sha. Don haka kada a rika tauna mai suga.

Mai gyambon ciki da ke yawan shan zuma ko za ta iya jawo masa matsala?

Daga Salisu A., Gombe

Amsa: E, a wani binciken kimiyya da aka yi a kasar Oman, wanda aka wallafa a mujallar Jami’ar Sarki kabusu a shekarar 2006 an gano cewa zuma za ta iya kashe kwayoyin da akan gani a cikin gyambon ciki wato H.pylori, sai dai zuma kala daya ce mai karfi wadda aka tabbatar za ta iya wannan aiki ba duka nau’o’in zuma ba. Sai dai ana so a fara da magungunan kashe kwayoyin cuta na asibiti domin ganin bayan kwayoyin cutar gaba daya. Don haka za ka iya sha domin dama zuma ba ta daya daga cikin abincin da akan hana mai olsa ci. 

Ni ina da olsa amma da na sha magani ta warke sai ta dawo. Ko mene ne dalili?

Muhammad Sani H.

Amsa: Ai masu ciwon olsa bangon cikinsu ne ba ya da kwari. Don haka idan suka sha magungunan da aka zayyana musu na tsawon watannin da aka diba musu, suka gama, tana warkewa, amma idan suka koma halayen da suka jawo gyambon tun da fari kamar shan sigari ko cin abinci mai sa gyambon ko barin ciki da yunwa kamar yin azumi, duk za su iya sawa a dawo gidan jiya.

Shin tabon da yake fitowa mutane a wurare kamar goshi da kafa saboda yanayi na zama ko na sallah ba zai iya zama wani ciwo daban ba?

Daga Khalid M. Kaduna

Amsa: E, irin wannan tabo a wasu dai za ka ga ya zama tabo sosai mai tsuro kamar ciwo, amma ba ya zama wani ciwo babba da za a damu da shi kamar daji, domin kwayoyin fatar wurin ne ke sakin sinadarai na collagen masu yawa a wannan wurin, ba wai rikidewa suke ba kamar yadda ake samu a ciwon daji.

Ina da matsalar mura wadda ko yaushe ko yanayin zafi ko na sanyi hancina daya a toshe daya a bude. Idan dayan ya bude sai dayan ya toshe. Wace shawara za a bani?

Daga Albaba Ado

Amsa: E, akwai masu irin wannan mura irin taka wadda ba ta da takamaimai lokacin tashi, kullum hanci a toshe. Masu irin wannan mura mukan ba su shawara su nemi likitan hanci da makoshi ya duba kogon hanci ya ga ko akwai ‘yar tiyatar da za a iya yi ko kuma magunguna ne za su sha abin ya lafa.

Muna so mu rika ba da gudunmowarmu a bangaren kiwon lafiya. Yaya za mu yi?

Daga Lawal Kaliko, Niger

Amsa: Kamar yadda muka sha fada, a wannan shafi muna maraba da gudunmowa da shawarwari a bangaren kiwon lafiya in dai rubutu ne na kimiyya. Za a iya aikowa a adireshin imel da aka rubuta a saman wannan shafi.