✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

Shekaru biyu da suka wuce an mini tiyata ta c/s. Bayan watanni kamar uku wurin ya burma aka sake dinkewa. To amma a yanzu ban…

Shekaru biyu da suka wuce an mini tiyata ta c/s. Bayan watanni kamar uku wurin ya burma aka sake dinkewa. To amma a yanzu ban a iya yin mika sosai kuma idan ina fitari sai na ji aikin kamar yana tokare mafitsara ta. Shi ne abin yake bani tsoro

Daga Mai Damuwa

 

Amsa: Tabbas wannan abin ban tsoro ne. To amma fa akwai mafita. Tunda kin ce sau biyu aka yi wannan aiki dole ki samu babban asibiti kamar asibitin koyarwa, ki je ki ga kwararre ko kwararriyar likitar mata ki musu bayani domin a duba irin barnar da ta auku da yanayin da mahaifar ta ke ciki, a miki bayani, su fada miki kuma mafita, domin kada ki zo ki sake yin juna biyu haihuwa ko ma wata tiyatar c/s din ta gagara.

 

Yarinyata ce ta yi zazzabi aka kara mata jini sau biyu cikin dan lokaci shi ne nake neman shawara, domin yayarta ma ba a dade da mata karin jini ba. 

Daga Buhari I.T

 

Amsa: E, tunda ka ce zazzabi ne zai wahala a ce ba zazzabin maleriya ba ne, domin shi ne lamba-wan wajen kawo zazzabi da karancin jini a yara, don idan ya yi kamari yana zuke jini. Duk da haka dai yana da kyau ka tambaye su a asibitin ko sun gano dalilan wannan karancin jini a aune-aunen da suka yi. Idan sun ce maka zazzabin maleriyar ne, to sauro kawai za ka yaka a gidanka kafin shi ya ci galaba a kanka.

 

Me ke kawo ciwon kunne a yara ‘yan watanni biyu? Yaro na ne ban ankara ba sai na ga diwa a kunnensa. Ya ya ake kiyaye kamuwa?

Daga Maryam Villiri

 

Amsa: Qwayoyin cuta ne ke kawowa yara ciwon kunne mai diwa, kuma kafin su fara yawanci sai kin ga sun dan yi tari da zazzabi. Wato kwayoyin cutar daga makoshi suke samu su shiga kunne ta wata ‘yar kafa. Hanyar kariya ita ce yawan tsabtar hannayenki ke uwar jariri ta hanyar yawan wanke su da ruwa da sabulu, da yawan kula da tsabtar bulunboti ko feeder, ta hanyar tafasawa a ruwan zafi a kullum, idan ana ba shi wani abu a feeder, wanda mu mun fi so ma a yi amfani da kofi da cokali masu tsabta wajen ciyarwa da shayar da jarirai, ba bulunboti ba. Idan kuma kika ga ya fara mura ko tari ki maza ki kai shi a ba shi magunguna kafin abin ya shiga kunne.