✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi

LAFIYAR  MATA DA YARA Amsoshin Tambayoyi Da suka shafi juna biyu Mene ne ya ke kawo ciwon baya ga mai juna biyu? Domin ni nakan…

LAFIYAR 

MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Da suka shafi juna biyu

Mene ne ya ke kawo ciwon baya ga mai juna biyu? Domin ni nakan yi ciwon baya duk lokacin da na same shi

Daga Mama Basma

Amsa: Abin da ke ciki ne ke kwanciya a kan kashin gadon baya shi ya sa wasu matan masu juna biyu kan ji gadon bayansu na ciwo musamman idan cikin ya kai watanni bakwai zuwa sama.

Me ke sa wasu mata idan suka samu juna biyu akan ga; yawan kwadayi kamar cin kankara, wasu kafuwansu su kumbura, wasu su rika zubar da miyau wasu kuma sun yi fari-fat?

Daga Haruna Muhammad, Katsina

Amsa: Abin da ya fi kawo yawan kwadayi irin su cin kankara da siminti da sauransu da jiki ya yi fari-fat a masu juna biyu shi ne karancin jini. Shi kuma kumburin kafa a mai juna iri biyu ne, akwai na lafiya akwai wanda ba na lafiya ba. Wato idan aka ga kumburin kafa a mai juna sai an yi aune-aune na musamman a ga ko na lafiya ne ko ba na lafiya ba. Abubuwan da aka fi bincika su ne hawan jini da ciwon jijjiga. Shi kuma yawan zubar da miyau saboda dalilai biyu ne; na sinadarai masu sa taruwar miyau da na girman ciki wanda kan tokaro kahon zuci ya sa ruwan acid da miyau taruwa da dawowa baki daga ciki.

Shin wankin ciki wai dole ne ga wadda ta yi barin cikinta ko kuwa?

Daga Bushira Bala, Gumel

Amsa: A’a ba dole ba ne sai an yi wa macen da ta yi bari wankin ciki, domin barin ai iri-iri ne. Akwai wanda cikin da mabiyiya sukan bare gaba daya, akwai kuma wanda cikin kawai ne ke barewa amma mabiyiyar komi kankantarta ta ki barewa. To a irin wannan yanayi matar ba za ta daina zubar da jini mai yawa ba. Idan aka yi hoton scanning za a ga yaron cikin ko mabiyiyar. To idan akwai wannan sai an yi wankin ciki. Idan kuma aka yi hoton cikin aka ga ba komai za a iya kyale matar ba sai an yi wankin ciki ba. A irin wannan yanayi ita da kanta za ta ce ma ta ga komai ya bare.

Ina da juna biyu amma da aka yi hoton scanning ba a ga komai ba. Ni kuma ina jin alamun juna biyu. Shi ne nake neman shawara

Daga H.A., Gumel

Amsa: E, akwai wani nau’in juna biyu a likitance da kan iya kawo irin wannan matsala a yi hoto ba a ga komai ba, amma kwararriya ko kwararren likitan mata ne zai iya gano shi ba karamin likita ba ko dan koyo, domin hoton scanning din ma na musamman ake yi a gano shi ba irin wanda aka saba gani na sa na’ura kan mara ba. Shawara ita ce ki tambayi likitan da kike gani ko akwai halin tura ki wajen kwararren likita a nan, ko a asibitin da ya dan dara wannan.