✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amma ya iya bayar da Carry Ober

  Wani malamin jami’a ne mai hannu daya ya shiga dakin darasi ya gabatar da laccarsa kan darasin Karin magana.Bayan ya gama karantar da su…

 

Wani malamin jami’a ne mai hannu daya ya shiga dakin darasi ya gabatar da laccarsa kan darasin Karin magana.
Bayan ya gama karantar da su darasin sai ya ce da daliban idan an fahimta, to kowa zai ba da misalin karin magana daya. Bayan wasu sun bayar sai aka zo kan wata daliba wadda ta daga hannu. Ya ce ta fadi nata: Sai ta ce “Hannu daya ba ya daukar jinka!”
Sai malamin ya yi shiru ya dube ta ya ce eh! Amma yana iya ba da ‘Carry ober’ (maimaita shekarar darasi) don ubanki!
Daga 09099886988