✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin man kadanya 5 ga fata

Wannan mai na magance kurajen fuska da gautsin fata da kuna da kuma kyasbi.

Man kade na da matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai da dama har da sinadarin bitamin A da E

Wannan mai na magance kurajen fuska da gautsin fata da kuna da kuma kyasbi.

Amfani da wannan man na sanya sulbin fata.

Ga kadan daga cikin amfanin man kade.

Hadin magance kyasbi

A samu man sandal da man labender a zuba a cikin man kade sannan a kwaba su sosai sai a samu kwalba a zuba hadin.

A mayar da wannan mai man shafawa a kullum.

A yi amfani da shi na tsawon wata shida za a ga canji.

Magance fata mai gautsi

 A samu man kwakwa da man zaitun da kuma man almond sannan a zuba a kwalba a kuma zuba man kade a ciki, sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan a rika shafawa a jiki.

A mayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.

Domin magance bushewar lebba

A samu zuma da man zaitun sai a zuba a kan man kade a kwaba su sosai.

Sai a sa a wuri mai sanyi. Sannan a rika shafawa a baki a kullum za a samu sauki.

Domin magance kurajen aski ga maza

A samu man rosemary da man kwakwa sannan a zuba a kan man kade a kwaba.

A rika shafawa a kulum bayan an aske gemu. Yana warkar da kurajen da suke fesowa a gemu bayan an yi aski.