✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 36 sun mutu 470 sun rasa muhallai a ambaliyar Sakkwato

Akalla mutane 36 ne suka mutu 470 kuma suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa a Sakkwato

Akalla mutane 36 ne suka mutu 470 kuma suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a jihar Sakkwato daga watan Janairun 2020 zuwa yanzu.

Daraktan wayar da kai da bayar da agaji na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Mustapha Umar shine ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan hanyoyin takaita bala’o’i a jihar day a gudana a Sakkwato ranar Alhamis.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ce dai ta shirya taron.

Mustapha ya ce akalla hektar gonaki kusan 302,500 ce ruwan ya tafi da ita yayin da sama da dabbobi 120 suka mutu a fadin jihar.

Ya kuma ce 19 daga cikin kananan hukumomin jihar 23 sun fuskanci matsalar ambaliyar a daminar bana.

Kazalika, shugaban hukumar NEMA ta kasa AVM Mahmud Muhammad mai ritaya ya ce an shirya taron ne da nufin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan hanyoyin magance matsalar domin a sami mafita.

Mahmud, wanda ya sami wakilcin shugaban ofishin hukumar a jihar, Dakta Kofoworola Soleye ya ce za su yi nazarin dukkan abubuwan da ake zargin sune ummul aba’isun matsalar a cikin shekarun da suka gabata.

A cewarsa, “Muna sa ran shirin ya bullo da nagartattun hanyoyi, shawarwari da kuma manufofi da za su takaita, tare da ankarar da jama’a kan kowacce irin annoba.

“Sauran bala’o’i kamar su guguwa, ambaliya, fari, kwararowar hamada, da kuma gobara da suke da illa ga tattalin arziki da harkar tsaro sun taka rawa sosai wajen kara dagula al’amura a Najeriya da kuma mayar da hannun agogo baya,” inji shugaban hukumar.

Daga nan sai ya yi kira ga dukkan hukumomi kan su bayar da dukkan hadin kan da ya kamata ga NEMA domin a gano bakin zaren.