Makonni kadan bayan farfadowar Pakistan daga ambaliya mafi muni a tarihin kasar, dalibai na dari-darin komawa makaranta.
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce kimanin makarantu 23,900 ne suka zamo sansanonin wadanda ambaliyar ta rusawa muhallai, da kuma halaka mutane 1719.
- ISWAP na shirin kaddamar da hari a Zamfara —Gwamnati
- Tinubu ya yi alkawarin hako mai da inganta tsaro a Arewa
Kazalika rahotanni sun bayyana cewa, fiye da rabin wadanda ambaliyar ta shafa sun fito ne daga Kudancin lardin Sindh.
A lardin dai, kimanin makarantu 12,000 ne ambaliyar ta rusa, lamarin da ya dakatar da karatun yara akalla miliyan biyu.
Mashawarcin Babban Ministan Ba da Agaji a lardin Sindh, Rasool Bux Chandio ya ce ambaliyar ta mamaye kashi daya bisa ukun kasar.
“Muna fargabar yara za su watsar da batun karatu su koma aikin karfi don samun abin kai wa bakin salati sakamakon daina zuwa makarantar.
“Dalibai mata ma muna fargabar hakan ya sa a yi musu auren dole,” in ji Gondal.
Ya kuma ce UNICEF ya kafa cibiyoyin karatu na wucin gadi guda 90, kasancewar yanzu haka kasar tafi kowacce yawan yaran da suka daina zuwa makaranta a duniya.
Alkaluma dai na nuna kimanin yara miliyan 22.8 ne masu shekaru biyar zuwa 16 ba sa zuwa makaranta, adadin da shi ne kaso 44 na duk yara masu wadannan shekarun a kasar.