✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliya ta hallaka ’ya’ya 4 da mahaifiyarsu a Anambra

Wani biyo yan nuna yadda ake fito da gawar matar da ’ya’yanta hudu da kuma ’yar uwarta daga gidan bayan iftila'in

Iyalin wani gida sun nutse a ruwa bayan ambaliya ta shafe gidansu a kauyen Nzam da ke Karamar Hukumar Anambra ta Yamma a jihar Anambra a ranar Talata.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta an ga mutane na fito da gawar matar da ’ya’yanta hudu da kuma ’yar uwarta daga gidan bayan iftila’in.

Muryar da ta dauki bidiyon ta bayyana cewa iyalin sun gama kwashe kayansu tsaf domin barin gidan kafin lamarin ya faru.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata mutane 81 suka rasu a hatsarin kwale-kwale guda biyu a karamar Hukumar Ogbaru ta jihar.

A hannu guda Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, a wani taron manema labarai da ta gudanar, ta ce ta fara amfani da jirage masu saukar ungulu domin ceto mazauna yankunan da ambaliyar ta rutsa da su.