Wanzu haka amaryar nan da ta yi batan dabo kwana biyu kafin aurenta a Kano ta dawo inda ta hadu da iyayenta a safiyar Talata.
Kawun amaryar, Gwani Yahuza Gwani Danzarga ya shaida wa Aminiya cewa wani mutum ne ya kira mahaifiyarta ya gaya mata cewa sun tsinci wata yarinya a kan Titin Jami’ar Bayero.
- ’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari
- Mutum 3 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi
- Za a yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya
“Ana sanar da mu cewa an ga wata yarinya a kan titin Jami’ar Bayero sai muka hanazarta zuwa wurin inda muka samu Amina tana zaune tana ta kuka,” inji shi.
A cewar Gwani Yahuza, duk da cewar sun samu ’yar tasu a wani hali na rashin magana, amma sun gode wa Allah da ganin ta da suka yi cikin koshin lafiya.
Ya ce a lokacin, “Ba ta iya magana sai dai ta yi nuni da hannunta, amma mun godewa Allah da yadda muka same ta Alhamdulillah.”
Wata majiya a iyalan amarya Aminya ta bayyana cewa an dage gudanar da bikin amaryar har zuwa lokacin da za ta kara murmurewa.
Tun a ranar Juma’a iyayen amarya Amina Gwani Danzarga suka bayayana labarin bacewarta a yayin da take dawowa daga unguwar Dorayi inda ta je ta kai wa wata kawarta katin jarrabawarta.